Gwamnan jihar Osun ya amince da biyan 1,887 kudin giratuti ga malaman da sukayi ritaya daga aiki

0
83

Gwamnan jihar Osun, Adegboyega Oyetola, ya amince da fitar da kudi N377,120,472.20, domin biyan ‘yan fansho, ya bayyana hakan ne a lokacin yaye daliban firamare karo na hudu.

An bayyana hakan ne a wata sanarwa da aka samu a Osogbo ranar Laraba kuma mai dauke da sa hannun shugaban ma’aikatan jihar, Dr. Festus Oyebade.

Sanarwar ta kuma ce a ranar Alhamis ne za a fara biyan wadanda suka amfana.

Ya kara da cewa, “jimillar wadanda suka amfana sun kai 1,887 a kan jimillar kudi N377,120,472.20.

“Za a sanya jerin sunayen ne a allunan hukumar fansho na karamar hukumar da ma’aikatar yada labarai da hulda da jama’a a yau Laraba 26 ga Oktoba, 2022.

“Za a fara biyan albashin gobe Alhamis 27 ga watan Oktoba 2022. Gwamnan ya tabbatar wa ma’aikatan jihar hakan ya kuma yi alkawarin samar musu da kayayayyakin jindadi da walwala a lokacin gwamnatin sa.”