HomeLabaraiZa a yi wa Buhari da gwamnoni karin albashi

Za a yi wa Buhari da gwamnoni karin albashi

Date:

Related stories

Sarkin Dutse Nuhu Sunusi ya rasu

Allah ya yi wa Sarkin Dutse Alhaji Dr. Nuhu...

Shin ko kunsan tsibirin da aka hana kowa zuwa a duniya ?

Shi wannan guri Mai suna North Sentinel Island an...

Mayakan ISWAP sun raba wa fasinjoji dubu dari-dari

Mayakan ISWAP sun rarraba wa fasinjoji da dama Naira...

Ya kamata mutane su yi amfani da kwanaki 10 wajen mayar da tsofaffin kudin su banki – Sanusi

Sarkin Kano murabus kuma Khalifan Tijaniyya, Sanusi Lamido Sanusi,...

‘Yan sanda sun bankado maboyar ‘yan bindiga, sun cafke mutum 6 a Nasarawa

Rundunar ‘yansandan Jihar Nasarawa ta ce ta kai farmaki...

Hukumar Tattarawa da Raba Kudin Shiga ta Kasa (RMAFC), ta ce ta kammala shirye-shiryenta don yin karin albashi ga Shugaban Kasa da mataimakinsa da gwamnoni da mataimakansu karin albashi.

Sauran sun hada da masu rike da mukaman siyasa da alkalai da wasu masu rike da mukaman gwamnati.

Shugaban RMAFC, Mohammed Bello Shehu ne ya ce lokaci ya dade da yi na karin albashi ga masu rike da mukaman siyasa da dangoginsu, saboda rabon da a yi hakan tun shekarar 2008.

Ya bayyana haka ne, yayin da ya ziyarci shugaban Kungiyar Gwamnonin Najeriya (NGF), Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na Jihar Sakkwato a ofishinsa da ke Abuja.

Sai dai kuma, da alama yunkurin hukumar RMAFC na yi wa ’yan siyasa da sauransu karin albashin bai yi wa Kungiyar Kwadago ta Najeriya (NLC) dadi ba.

Domin kuwa, kungiyar ta ce mafi karancin albashi na N30,000 da ake biyan ma’aikatan gwamnati bai taka kara ya karya ba idan aka kwatanta da makudan kudaden da ake biyan ’yan siyasar kasar nan.

NLC ta ce ma’aikatan gwamnati a matakin kasa da jihohi da kananan hukumomi ne suka cancanci samun karin albashi, musamman idan aka yi la’akari da kalubalen tattalin arziki gami da tsadar rayuwar da ake fuskanta.

Bello ya ce dokar kasa ce ta bai wa RMAFC ikon yanka albashin da za a rika biyan ’yan siyasa da masu rike da mukaman gwamnati da kuma ma’aikatan fannin shari’a.

Subscribe

- Never miss a story with notifications

- Gain full access to our premium content

- Browse free from up to 5 devices at once

Latest stories