An ceto ’yan sandan da aka yi garkuwa da su a Kuros Riba

0
210

Rundunar ’yan Sandan jihar Kuros Riba ta tabbatar da ceto wasu jami’anta uku wadanda matasan yankin Ndon Owong, cikin Karamar Hukumar Odukpani a jihar suka yi garkuwa da su.

Mai magana da yawun rundunar, SP Irene Ugbo, ta ce dakarun rundunar yaki da kungiyar asiri a jihar ne suka ceto jami’an a ranar Litinin.

Ta kuma shaida wa Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN), ranar talata cewa, an kama mutum biyu daga cikin wadanda ake zargi da yin garkuwa da jami’an.

Ndon Owong yanki ne mai fama da ayyukn matsafa wanda a cewar ta, hukuma ba za ra zuba ido ta kyale ana salwantar da rayukna jama’a ba.