Home Labarai CBN ya ba da wa’adin kwana 47 a mai da tsoffin kudin...

CBN ya ba da wa’adin kwana 47 a mai da tsoffin kudin da za a sauya banki

0
123

Sakamakon matakin da babban bankin Najeriya ya dauka na sauya fasalin wasu takardun kudin kasar, an umarci al’ummar kasar da su mayar da tsoffin kudaden da za a sauya zuwa banki.

CBN, ya ce idan mutane suka mayar da kudaden ba tare da bata lokaci ba, to za su iya samun musayar kudinsu a kan kari.

Ya ce saboda wannan sabon tsarin yanzu an cire duk wani caji da ake yi a kan kudin da ake kai wa bankuna ba tare da bata lokaci ba, kuma duk yawan kudin.

To sai dai kuma masana tattalin arziki a Najeriya, sun yi tsokaci a kan wa’adin mayar da tsoffin kudin da za a sauya zuwa banki.

Aliyu Da’u, masanin tattalin arziki ne a Najeriya, ya shaida wa BBC cewa, wa’adin da babban bankin na Najeriya a gaskiya ya yi kadan bisa la’akari da yawan kudin da ke hannun mutane.

 Ya ce,” Idan aka yi la’akari da kwanakin da aka diba na mayar da wadannan kudade gaskiya sun kadan, domin dole za a samu cunkoson mutanen da za su je bankuna don mayar da kudinsu.

Ga batun cutar korona wadda har yanzu akwai ta, kuma duk in da aka samu cunkoson mutane idan har akwai mai ita ai dole a yadata, sannan ga batun hadarin da ake akwai na mutane na kan layin shiga banki barayi su dirar musu su kwace kudin.”

Masanin tattalin arzikin, duk wadannan matsaloli ne da za a iya fuskanta saboda takaitaccen lokacin da aka bayar na mayar da wadannan kudade.

Aliyu Da’u, ya ce,” Baya ga wadannan matsaloli, akwai kuma fargabar da mutane ke da ita cewa batun sauya kudaden nan zai iya durkusar da jarin wasu musamman ‘yan kasuwa.”

Ya ce, to amma tun da CBN ya ce a mayar da kudin don sauyawa, to ba mamaki akwai wasu bayanai na sirri da gwamnati ke da shi wanda jama’ar gari ba su dashi, kamar batun ‘yan siyasar da suka tara kudi suka ajiye don ayi amfani da su a lokacin zabe.

To ba mamaki an bayar da wannan takaitaccen lokaci ne don a samu damar karbe kudaden daga wajen ‘yan siyasa wata kila a samu saukin raba kudi a loakci zabe.

 Masanin tattalin arzikin ya ce, bayan siyasa akwai kuma batun ‘yan bindiga d ake satar mutane don kudin fansa, ba mamaki suma suna da irin wadannan kudade da za a sauya, to idan har aka bayar da wannan wa’adi ai dole su rabu da su don sauyawa.

 Ya ce, to idan aka yi la’akari da irin wadannan misalai, a iya cewa matakin sanya wa’adin ya yi dai-dai, to amma kuma a hakikanin gaskiya lamarin zai shafi mutane sosai musamman ‘yan kasuwa.

 A ranar Laraba ne babban bankin Najeriyar ya sanar da matakin sauya fasalin kudin kasar daga takardar naira 100 zuwa 1000, in da ya buƙaci masu kuɗi a hannu su mayar da su bankuna cikin ƙasa da kwana 50.

 Kazalika CBN din, ya ce sabbin kudaden da za a samar za su fara yawo a hannun mutane daga ranar 15 ga watan Disambar 2022, sannan kuma za a ci gaba da amfani da tsofaffin kudaden har nan da ranar 31 ga watan Janairun 2023.

X whatsapp