NNPC da rukunin kamfanin Daewoo sun kulla yarjejeniyar gyaran matatar mai ta Kaduna

0
66

Kamfanin Mai na NNPCL ya kulla yarjejeniyar gyaran Matatar Mai ta Kaduna da kamfanin Daewoo Group na kasar Koriya ta Kudu.

NNPCL da Deawoo Group sun sanya hannu kan yarjejeniyar ne a daidai lokacin da Najeriya ke jiran fara aikin Matatar Mai ta Warri a watannin shidan farkon shekarar  2023, bayan gyare-gyaren da kamfanin ya yi masa.Shugaban Kamfanin NNPCL, Mele Kyari, ne ya sanya hannu kan yarjejeniyar ta gyaran Matatar Man ta Kaduna a ranar Alhamis, a birnin Seoul na kasar Koriya ta Kudu.

Shugaba Muhammadu Buhari, ya bayyana wa taron sanya hannun burinsa na ganin an, “Kammala ayyukan matatun man Warri da Kaduna da kuma jiragen dakon iskar gas.

“Tabbas hakan zai bayar da karin dama ga Daewoo da sauran kamfanonin kasar Koriya ta Kudu a Najeriya.”

Fadar Shugaban Kasa ta Ruwaito shi yana cewa, “Na san Daewoo Group babban kamfani ne da ke gudanar da harkokinsa a bangaren motoci da sufurin jiragen ruwa da sauran bangarori.

“Yanzu haka kuma yana kera jiragen kasan dakon iskar gas na Najeriya da kuma kera wa NNPC da kawayensa jiregen ruwan dakon gas.”

Buhari, ta bakin kakakinsa, Femi Adesina, ya ce, “Ina kuma godiya bisa kwarin gwiwa da kuke da shi a kan Najeriya,”  in ji Shugaba Buhari ga kamfanin.

Shugaban kasar da jami’an gwamnatin Najeriya sun je Koriya ta Kudu ne domin halartar taron farko kan sarrafa tsirrai na duniya da aka gudanar a kasar.