’Yan kasuwar da za a cefanar wa da filayen jiragen saman Najeriya

0
55

Gwamnatin Tarayya ta sanar da ’yan kasuwar da ta zaba don cefanar musu da filayen jiragen saman kasar nan.

Ministan Sufurin Jiragen Sama, Sanata Hadi Sirika ne ya shaida wa manema labarai haka ran Laraba a Abuja.

A cewar ministan, filayen jiragen saman da za a cefanar sun hada da na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja da na Murtala Mohammedda ke Legas da kuma na Malam Aminu da ke Kano.

Sannan ya lissafo kamfanonin da suke kan gaba wajen sayen filayen jirgin, da suka hada da Corporacion America Airports Consortium da TAV/NAHCO/Project Plant Limited da kuma Corporacion America Airports Consortium da sauransu.

Ministan ya ce, har zuwa karewar wa’adin da aka bude kofa ga masu sha’awar filayen, babu wani kamfani da ya nuna sha’awarsa a kan Babban Filin Jirgin Sama na Fatakwal.

Sirika ya ce, matakan da akan bi wajen cefanar da filin jirgin sama yawa gare su, kuma gwamnati za ta yi komai a fili don kowa ya shaida.