Ganduje ya kaddamar da manyan motocin sufuri 100 da kanana 50 a Kano

0
54

Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya kaddamar da manyan motocin zirga-zirgar jama’a a birnin Kano guda 100 da kanana 50.

Bikin wanda aka gudanar a ranar Lahadi, an yi shi ne da nufin magance kalubalen sufurin da ke addabar jama’ar Jogana da Yankura zuwa garuruwan dake kan hanyar Janguza.

Motocin bas 100 da kanana 50 din da aka yi musu fentin kore da ratsin fari za su fara aiki ne nan take.

Da yake jawabi a wajen bikin, Gwamna Ganduje, ya ce gina wa da kuma fadada hanyoyi da dama, samar da gadar sama da na karkashin kasa da sauran ababen more rayuwa da dama sun zama wajibi yin su a birnin  na kano mai taken  kasuwanci da sana’o’i.