Shugaban kasar Ghana Nana Akufo Addo ya bayyana cewa kasar na fama da matsin tattalin arziki mafi muni a tarhi.
A wani jawabi da ya yi ta kafar talabijin ɗin ƙasar a jiya Lahadi, Shugaba Addo ya bayyana cewa suna cikin matsala.
Darajar kuɗin ƙasar ta ragu da kashi 50 cikin 100 a bana kuma an saka kuɗin kasar a jerin kuɗaɗen duniya da darajarsu ta fadi.
Shugaban kasar ya ɗora alhakin faɗuwar darajar kuɗin na sidi kan yaɗa jita-jita, da kuma ƴan kasuwar canji na bayan fage inda ya ce babban bankin ƙasar a shirye yake ya yi dirar mikiya kan waɗanda ke da hannu a wannan lamari.
Farashin mai na ci gaba da tashi a ƙasar kuma an samu hauhawar farashi da kashi 37 cikin 100.
Cikin matakan da shugaban zai ɗauka, har da rage kashi 30 cikin 100 na albashinsa da mataimakinsa da ministoci da wasu masu riƙe da muƙaman gwamnati.