Rahama Sadau ta zama gwarzuwar finafinai ta Afirka

0
289

Fitacciyar jarumar Kannywood, Rahama Sadau ta lashe kambun Gwazuwar Jarumar Afirka a taron karrama ’yan fim da aka yi a birnin Toronto na kasar Canada.

Jarumar ce ta bayyana haka a shafukanta na sada zumunta, inda ta ce, “Na lashe kambun Gwarzuwar Jarumar Afirka a taron karrama ‘yan fim na duniya na bangaren Nollywood.

“Tun farko da na ga sunana, sai ya sa a raina a cewa wannan ma kadai ya isa abin murna. Ashe in ce zan lashe kambun.

“Ina godiya ga ubangidana, AY mai wasan barkwanci domin wannan damar da ya ba ni, da Toka Mcbaror bisa namijin kokarinsa kamar kullum.

Wannan nasarar ba za ta samu ba, ba tare sa fasahar kirkirarka ba. Ina taya murna ga dukkan wadanda muka yi aiki da su.

“Ina tsimayin lokacin da mutanen duniya za su kalli fim din Almajiri.”

Jarumar ta lashe kambun ne bisa rawar da ta taka a fim din Almajiri da darakta Toka Mcbaror ya shirya da harshen Ingilishi sannan aka yi amfani da jaruman Kannywood da na Nollywood.