’Yan bindiga sun sace mutum 6 a wata unguwa a Zariya

0
118

Wasu da ake zargin ’yan bindiga ne sun kai hari Unguwar Kofar Gayan da ke Karamar Hukumar Zariya inda suka yi awon gaba da mutane shida a ranar Lahadi da daddare.

Wata majiyar jami’an tsaro ta sanar da Aminiya cewa, maharan sun afka Unguwar ce da misalin karfe 11.30 na dare inda suka rika harbe-harbe kafin daga bisani su dauke mutane shidan.

Majiyar ta bayyana wasu daga cikin mutanen da aka dauke sun hada wasu ma’aurata – Khalifa Ibrahim da matarsa Karima Khalifa, da wani malamin addini; Abdulkadir Alaramma, Idris Musa da kuma wani Ikira Isiyaku.

Duk kokarin tuntubar Jami’in rundunar ’yan sandan Jihar Kaduna Mohammed Jalinge ya ci tura, sakamakon rashin samun wayarsa a lokacin hada wannan rahoto.

’Yan Unguwar Kofar Gayan dai sun dade suna fama da hare-haren ’yan bindiga a ’yan shekarun nan, inda suka rika fuskantar sace-sacen mutane akai akai.

Wakilinmu ya ruwaito cewa, a unguwar ce aka taba dauke wani jami’in Hukumar Kwastam wanda ya shafe kwanaki 69 a hannun maharan, wanda daga bisani suka sako shi bayan karbar kudin fansa.

Unguwar Kofar Gayan ce dai matsugunar Babban Asibitin Gambo Sawaba da ta kunshi gidaje masu saukin kudi da ake kira Lowcost.