Za mu kawo karshen matsalar tsaro a wata 6 in muka ci zabe – Kashim Shettima

0
115

Dan takarar Mataimakin Shugaban Kasa na jam’iyyar APC, Kashim Shettima ya yi alkawarin za su kawo karshen matsalar tsaron Najeriya cikin wata shida muddin aka zabi Bola Tinubu a matsayin Shugaban Najeriya a 2023.

Ya bayyana hakan ne yayin wani taron fahimtar juna da ya gudana tsakanin dan takarar da ’yan kasuwar jihar Legas ranar Talata.

A cewarsa, “Cikin wata shidan shekararmu ta farko idan aka zabe mu, Shugabana [Tinubu] zai yi duk ami yiwuwa wajen kawo karshen wannan rashin mutuncin da ya dame mu.”

Shi kuwa a nasa bangaren, Tinubu ya ce muddin ya ce zabe zai tabbatar an kara daukar mutane masu yawa aikin jami’an tsaro a matsayin daya daga cikin hanyoyin dawo da tsaro.

Tinubu ya kuma ce, “Za mu dada dibar mutane ayyukan jami’an tsaro kuma za mu tabbatar da inganta ayyukansu.

“Ta hanyar daukar wadannan matakan, za mu tabbatar da ganowa, zakulowa tare da ganin bayan duk wasu miyagun da suka addabe mu. Ba za su sake numfasawa ba har sai sun mika wuya,” inji shi.

A shekarar 2021 dai yayin wani taron bikin murnar zagayowar ranar haihuwarsa, Tinubu ya ba da shawarar daukar matasa miliyan 50 aikin soji don kawo karshen matsalar, maganar da ta tayar da kura sosai.

To sai dai daga bisani Kakakinsa, Tunde Rahman, ya ce tuntuben harshe aka samu, 50,000 maigidan nasa yake nufi, ba miliyan 50 ba.