Home Labarai An harbi tsohon firaministan Pakistan Imran Khan a zanga-zanga

An harbi tsohon firaministan Pakistan Imran Khan a zanga-zanga

0
51

An harbi tsohon Firaministan Pakistan Imran Khan a wani yunƙuri na kashe shi yayin da suke tsaka da zanga-zanga.

‘Yan jam’iyyarsu ta PTI sun ce an jikkata wasu mutum huɗu a ranar Alhamis, amma ba a kashe kowa ba.

Babu tabbas game da inda aka harbe shi – a ƙafa ko a hannu – amma wani mai taimaka masa na musamman ya ce ba ya cikin haɗari sosai.

Mista Khan mai shekara 70, na jagorantar maci ne zuwa Islamabad babban birnin ƙasar da zimmar neman a gudanar da zaɓe bayan an sauke shi daga kan mulki.

Wani babban hadiminsa ya faɗa wa kamfanin labarai na AFP cewa: “Yunƙurin kashe shi aka yi, a yi masa kisan gilla.”

An kama wani mutum da ake zargi, a cewar gidan talabijin na Geo da ke Pakistan.

A watan da ya gabata hukumar zaɓen Pakistan ta haramta masa sake riƙe muƙamin siyasa, sai dai tsohon tauraron ƙwallon kirket ɗin ya ce manaƙisa ce irin ta siyasa.

An zarge shi da ƙin bayyana haƙiƙanin kyautukan da ya samu daga ƙasashen waje da kuma ribar da ya samu daga cinikin kayan. Kyautukan sun ƙunshi agogunan Rolex, da zobe da maɓallin hannu na riga (links).

X whatsapp