Canjin Naira: EFCC ta dana wa gwamnoni tarko – Bawa

0
76

Hukumar Yaki da Masu Karya Tattalin Arziki kasa (EFCC) ta fallasa yadda wasu gwamnoni da ke shirin yin almundahanar biliyoyin kudade ta hanyar biyan albashin ma’aikata ta kan tebur.

Shugabna EFCC, Abdulrasheed Bawa, ya shaida wa Aminiya a wata hira ta musamman cewa, gwamnonin sun shirya yin hakan ne a matsayin daya daga cikin dabarunsu na kawar da haramtattun biliyoyin takardun Naira da ke makare a hannunsu.

“Bayanan sirri da muka samu sun gano wasu gwamnoni da suka ajiye makudan kudade a gidajensu da sauran wuare, yanzu suna kokarin su biya albashi a kan tebur,” in ji Bawa.

Ya bayyana cewa, gwamnonin da Hukumar take bibiya sun hada da wasu biyu daga yankin Arewa, na ukunsu kuma daga Kudu.

Aminiya ta tambaye shi ko EFCC za ta gayyaci gwamnonin su amsa tambayoyi, inda ya kada baki ya ce hukumar tana bibiyar lamarin sosai.

Ya ce, “Dole mu hana su kuma muna kan aiki, amma ba su riga sun biya albashi da kudaden ba tukuna.

“Amma wannan babban lamari ne,” domin ya saba Sashe na 2 na Dokar Haramta Safarar Kudade.

“Dokar a bayyane take: Duk mutumin da zai yi harkar kudi na sama Naira miliyan biyar a wata cibiyar kudi ya haramta; na kamfanoni da hukumomi kuma kada ya wuce N10m.

“Me ya sa sai yanzu kwatsam za su kirkiri biyan albashi a kan tebur, bayan a baya ta banki suke biyan ma’aikata?

“Za su bullo da dabaru iri-iri, za su yi kokarin tantance jami’ai da sauransu,” in ji shugbana na EFCC.

Ya kara da cewa hukumar za ta ci gaba da kai wa cibiyoyin ’yan canji samame a yunkurinta na dakile masu rike da haramtattun kudade da ke fadi-tashin rabuwa da su ta hanyar mayar da su kudaden kasashen waje.