INEC ta turo sabon kwamishinan zabe jihar Kano

0
100

Hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta, ta turo Ambassador Abdu Abdussamad Zango, a matsayin sabon kwamishinan zabe na jihar Kano.

Shugaban hukumar ta INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, wanda ya jagoranci bikin rantsawar  a ranar Alhamis a shalkwatar  Hukumar INEC da ke Abuja, ya gargadi sabbin kwamishinonin da su guji kai yawan ziyara gidajen gwamnatocin jihohin da aka tura su, domin kare mutuncinsu.

Idan dai ba  a manta ba a watan Yuli ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mika sunayen mutane 19 da aka nada a matsayin kwamishinoni a hukumar  INEC ga majalisar dattawa domin tantancewa.