Arsenal ta koma saman teburin firimiyar Ingila bayan doke Chelsea

0
78

Arsenal sun koma saman teburin gasar Firimiyar Ingila bayan da suka doke Chelsea da ci daya mai ban haushi a Stamford Bridge ta wajen kwallon da dan wasan bayansu, Gabrielya ci.

A cikin minti na 63 ne Gabriel ya saka kwallo a raga bayan da masu masaukin bakin suka gaza tare kwallon da Bukayo Saka ya kawo daga bugun kusurwa.

Sun samar da damammakin cin kwallaye a zubin farko na wasan, inda Martinelli da Gabriel Jesus suka zubar da su.

Chelsea, wanda tsohon dan wasan Arsenal da suka sayo, Pierre-Emerick Aubameyang ya gaza tabuka abin kirki a wasan na jiya Lahadi sun yi ta kokari abin ya ci tura, kuma yanzu haka wasanni 4 na gasar Firimiya kenan suka buga a jere ba tare da nasara ba.

A ranar Asabar ce Arsenal suka rasa matsayisu na Lamba 1 a teburin gasar Firimiya, bayan da Manchester City da suka karkare wasa da mutane 10 suka doke Fulham 2-1.