Tinubu ba shi da lokacin zuwa tarukan muhawara – APC

0
108

Kwamitin yakin neman zaben dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC Bola Tinubu, ya ce dan takarar ba shi da lokacin yawon halartar tarukan muhawara.

Jami’iyyar ta sanar da haka ne a martaninta ga korafin da ake yi na rashin halartar dan takarar taron muhawara da gidan talabijin na Arise ya shirya a Legas da ya janyo ce-ce-ku-ce.

Sanarwar, wacce daraktan yada labarai na kwamitin yakin neman zaben dan takarar, kuma Minista a Ma’aikatar Kwadago Festus Kiyamo ya sa hannu, ta ce, Tinubu na ganawa ne da jama’a kaitsaye.Keyamo ya kuma ce, kafofin yada labarai da yawa sun nuna sha’awarsu ta shirya irin wannan muhawara, kuma dan takarar bai zabi ya amsa gayyatar wasu ba, sannan ya kuma kyale wasu.

“Sannan tsarin yawon kamfe da ganawa da jama’a ba zai ba dan takararmu damar amsa gayyatarku ba domin guje wa zargin bambanci idan ya zo wannan bai je na sauran ba,” in ji Kiyamo.

Gidan talabijin na ARISE ya shirya muhawarar ce da hadin gwiwar Cibiyar Kula da Cigaban Dimukuradiya (CDD) domin ’yan takarkarar jam’iyyu su fada wa jama’a abin da za su yi idan sun zama shugaban kasa.

An yi taron muhawarar amma Tinubu da Atiku ba su samu damar halarta ba.