Gwamnatin APC ta yaudari ‘yan Najeriya – Kwankwaso

0
96

A ranar Laraba ne dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP, Sanata Rabi’u Kwankwaso, ya ziyarci Abakalaiki, babban birnin jihar Ebonyi a wata ziyara da yake kaiwa jihohi daban-daban domin yakin neman zabe gabanin zaben shugaban kasa na 2023 dake qaratowa a kasar.

Kwankwaso wanda ya samu rakiyar wani dattijon kasa, Alhaji Buba Galadima, ya kaddamar da ofishin yakin neman zaben jam’iyyar a kan babban titin Sabuwar Kasuwa ta Abakalaiki.

Daga bisani, ya ziyarci gwamnan jihar Ebonyi, David Umahi a masaukin shugaban kasa, tsohon gidan gwamnati da ke Abakalaiki.

Kwankwaso ya ci gaba da cewa shi da Umahi ba su ji dadin jam’iyyar PDP ba, shi yasa suka yanke shawarar barin jam’iyyar sabida kura-kuran da jam’iyyar ke tafkawa.

“NNPP ita ce jam’iyyar da za ta yi nasara a Arewa saboda. Gwamnatin APC ta yaudari ‘yan kasa. Mun yi farin ciki matuka yadda ’yan takara masu muhimmanci ba su samu tikitin jam’iyyunsu ba”.

 Kwankwaso ya ci gaba da cewa, abin da kasar nan ke bukata shi ne wanda ya cancanta, kwararre, mai rikon amana da kuma karfin da zai iya mayar da al’ummar kasar nan tudun mun tsira.