INEC ta samar da tsarin yadda ‘yan gudun hijira za su yi zabe a Zamfara

0
117

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta (INEC) a Jihar Zamafara ta sanar da cewar ta samar da tsarin yadda ‘yan gudun hijira da kuma al’ummar da hare-haren ‘yan bindiga ya kore su, za su kada kuri’unsu a zaben 2023.

Kwamishinan hukumar a jihar, Farfesa Sa’idu Ahmad ya sanar da hakan a hirarsa da manema labarai a jihar a kan shirye-shiyen da hukumar ke yi na fara lika sunayen masu jefa kuri’a a jihar.

A cewar Farfesa Ahmad, rashin tsaro ya janyo wa hukumar rashin fara gudanar da ayykanta na shirye-shiyen zaben a kan lokacin da ya dace kafin zuwan zaben na 2023, inda ya ce hakan ya zamowa hukumar babban kalubale wajen shiga lungu da sako na jihar don yin rijistar masu karbar katin zabe, musamman saboda kalubalen rashin tsaro.

kwamishinan ya ce duk da wannan kalubalen na rashin tsaron, hukumar ta samu nasarar yi wa adadin wadanda suka kai munzalin jefa kuri’a guda 211,970 a jihar.

Ya kara da cewa “Muna da kididdigar, musamman a kananan hukumomin 13 zuwa 14, akwai mutanen da dama da hare-haren na ‘yan bindiga ya tilasta su tashi daga yankunansu.

 Farfesa Sa’idu ya kuma bayyana cewa, hukumar ta fara karbar kayan gudanar da zaben masu muhimma ci domin gudanar da zabukan 2023.

Ya sanar da cewa, hukumar ta kuma magance yin rijistar katin zabe fiye da daya, inda ya ce, hukumar za ta kuma kafe sunayen masu jefa kuri’a daga ranar 12 ga watan Nuwamba 2022 zuwa ranar 19 ga watan Nuwamba, 2022.