Mutane 28 sun mutu a rikicin kabilanci tsakanin al’ummomin Benue da Ebonyi

0
51

Rahotanni daga Najeriya na cewa akalla mutane 28 ne aka kashe a karamar hukumar Ado ta jihar Benue mai iyaka da jihar Ebonyi, sakamakon wani rikicin kabilanci tsakanin al’ummomin jihohin biyu masu makwabtaka da juna.

Mazauna yankin sun ce akasarin wadanda aka kashe mata ne da kananan yara, bayan da aka sake fardado dadaddiyar takun tsaka tsakanin kabilun jihohin biyu.

Shugaban Karamar Hukumar Ado, James Oche, wanda ya tabbatar wa manema labarai faruwar lamarin a Makurdi, ya ce rikicin ya barke ne sakamakon lalata wani wurin ibadar gargajiya na  al’ummar Ebonyi.

Ya ce an shiga bai wa hammata iska ne lokacin da wasu gungun mutaane da bata wannan wuri na ibadar gargajiya a Ebonyi ya wa ciwo suka dauki doka a hannu, inda suka afka wa al’ummar kaauyen Ezza a jihar Benue.

Oche ya ce wannan rikilci ya yi sanadin lalacewar kasuwa mafi girma a Ezza gaba daya, inda ya kara da cewa yanzu haka jami’an tsaro na sintiri a yankin don tabbatar da kaawo karshen rikicin.