Akalla ‘yan Najeriya 8 ne suka samu nasarar lashe mukaman da suka yi takara a kansu, yayin zaben tsakiyar wa’adin gwamnati da ya gudana a daren Talata a jihohin Georgia, Pensylvaniya da Minnesota a Amurka.
Shugabar hukumar kula da ‘yan Najeriya dake kasashen waje, Abike Dabiri-Erewa ta wallafa labarin a shafinta na Twitter.
Cikin sakon na ta na Twitter, shugabar hukumar ta NDC da aka kafa domin ‘yan Najeriya da ke kasashen ketare, ta taya wadanda suka lashe zaben murna kan nasarar da suka samu.
‘Yan Najeriyar da suka yi takara tare da samun nasara a zaben tsakiyar wa’adin gwamnati a Amurka, sun hada da, Segun Adeyinka, Gabe Okoye, Solomon Adesanya, Tish Naghishe, Phil Olaleye, Carol Kazeem, Oye Owolewa da kuma Esther Agbaje.
A halin yanzu ‘yan takarar sun zama ‘yan majalisar wakilai a kasar ta Amurka, karkashin inuwar jam’iyar Demokrat mai mulki, wadanda ke zaman jiran kama aikin wakilcin jihohin nasu.
A ranar talatar da ta gabata aka gudanar da zaben tsakiyar wa’adin gwamnatin Amurka, kuma a nan gaba za a sanya ranakun da za a karasa zaben, domin cike guraben mukaman da aka gaza samun wanda ya samu rinjayen kuri’u a yayin takarar da aka yi akansu.