Iran ta kera makami mai linzami da ke ratsa kowanne irin tsaro

0
60

Iran ta ce ta kera wani makami mai linzami mai matsanancin gudu da ka iya ratsa duk wani tsarin tsaro da aka shimfida, kamar yadda babban kwamandan rundunar juyin juye hali ta kasar Amirali Hajizadeh ya bayyana a yau Alhamis.

Wannan shu’umin makami ma linzami, kamar sauran makamai masu cin dogon zango, yana da gudun da ya ninka sauti har sau 5.

Hajizadeh ya ce an yi wannan makami ne don iya waske duk wani tsari na tsaron makami mai linzami, inda ya kara da cewa zai dau gwamman shekaru kafin a samar da wani tsarin tsaro da zai dakile shi.

Wannan sanarwar na zuwa ne kwanaki bayan da iran ta amsa zargin cewa ita ta bai wa Rasha jirage marasa matuka, amma ta musanta  cewa ta bada jiragen ne bayan mamayar Ukraine.

Akasin makami mai cin dogon zango, wannan makami mai linzami yana tafiya ne a kasa kasa da sararin samaniya, lamarin da ya sa yake iya kai wa ga inda aka harba shi da wuri.

Gwajin irin wannan makami da Korea ta Arewa ta yi a shekarar da ta gabata ya haddasa damuwa a kan rige rigen samun makamancin makamin.

A yayin da kasashe kamar su Amurka suka samar da na’urori da ke bada kariya ga makami mai linzami da ke cin dogon zango, taka wa wannan shu’umin makami birki na da matukar wahala.