Kotu ta kori Sanatan Taraba daga kujerarsa saboda sauya sheka zuwa APC

0
66

Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Jalingo a Jihar Taraba, ta kori Sanata Emmanuel Bwacha daga kujerarsa ta majalisar dokoki, bisa zargin ficewa daga jam’iyyar PDP zuwa jam’iyyar APC.

Bwacha shi ne Sanata mai wakiltar Taraba ta Kudu a majalisar dokokin kasar nan.

Jam’iyyar PDP a Jihar Taraba tun bayan ficewar Bwacha daga jam’iyyar zuwa APC ta garzaya kotu domin bayyana kujerar Sanatan a matsayin wanda ba kowa a cikinta saboda ficewa daga jam’iyyar da aka zabe shi.

Mai shari’a Simon Amobeda a hukuncin da ya yanke ya umarci Sanata Bwacha da ya gaggauta barin kujerarsa a majalisar dattawa.