Ganduje ya ware naira miliyan 300 zai biya kudin karatun daliban Kano da ke karatu a waje

0
103

Gwamnan jihar Kano, Dakta Umar Ganduje, ya amince da sakin Naira miliyan 300 a matsayin kudin karatu ga dalibai ‘Yan asalin jihar Kano da gwamnati ta dauki nauyin karatu a jami’ar Near East University, Cyprus.

Kwamishiniyar ilimi mai zurfi, Dokta Mariya Mahmoud Bunkure, ta bayyana hakan.

Dokta Bunkure ta ce biyan kudin makarantar yana cika alkawarin da Gwamna Ganduje ya yi musanman saboda daukaka martabar zamantakewa da tattalin arzikin matasan jihar ta hanyar samar da ingantaccen ilimi a kan lokaci.

Kwamishinan ta gode wa gwamnan da ya tabbatar da mafarkinta.

Ta taya daliban da iyayensu murnar samun irin wannan gagarumin tallafi tare da bukatarsu da su yi kyakkyawan amfani da ilimin da suka samu wajen ci gaban jihar Kano da ma Nijeriya baki daya.