Kona ofishin zabe: INEC ta kira taron gaggawa da hukumomi tsaro

0
75

Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), ta kira ɓangarorin jami’an tsaro zuwa taron gaggawa domin tattauna hanyoyin hana ci gaba da cinna wa ofisoshin hukumar zaɓe wuta.

Taron wanda Kakakin Yaɗa Labarai na INEC, Festus Okoye ya sanar cewa ya gudana a ranar Juma’a, an tattauna matsalar hare-haren da aka kai ne sau biyu a cikin kwanaki biyu jere a jihohin Ogun da Osun.

Okoye ya ce an gayyaci dukkan ɓangarorin da ke cikin Kwamitin Kula da Harkokin Tsaron Zaɓe (ICCES) domin tattauna matsalar, ganin yadda ranakun fara zaɓen sai kusantowa su ke yi.

“Mun samu labarin hare-haren banka wa ofisoshin INEC wuta har wurare biyu a jihohin Ogun da Osun. Wannan abu kuwa abin damuwa ne matuƙa.

“Kwamishinan Zaɓe na Jihar Ogun, Niyi Ijalaiye ya sanar da cewa an kai wa ofishin INEC da ke Ƙaramar Hukumar Abeokuta ta Kudu harin da aka banka masa wuta.

“Maharan sun cimma mummunan burin su bayan sun fi ƙarfin jami’an tsaron da ke wurin, inda su ka banka wa ginin wuta.

“Daga cikin kayayyakin da aka yi asara akwai akwatin zaɓe 904, rumfar shiga a yi zaɓe 29, jakunkunan zuba kayan zaɓe 57, janareto takwas da kuma katin shaidar rajistar zaɓe 65,699 na waɗanda ba su kai ga karɓar na su ba,” inji Okoye.

Haka kuma ya ƙara da cewa an yi irin wannan harin banka wa ofishin INEC wuta a ranar Alhamis, “a Karamar Hukumar Ede ta Kudu, cikin Jihar Osun, kamar yadda Kwamishinan Zaɓe na Jihar, Mutiu Agboke ya sanar.”

Sai dai ya ce a nan ɓarnar ba ta yi muni ba kamar ta Jihar Ogun. Kuma ya ce a wannan ba a ƙone muhimman takardu da katin shaidar rajistar zaɓe, kamar yadda aka yi a Ogun ba.

Yayin da ake saura kwanaki 106 a fara zaɓe, Okoye ya ce tuni INEC ta fara aikawa da kayan zaɓe a ofisoshin ta jihohi daban-daban a ƙasar nan. Dalilin haka ne ya bayyana cewa hare-haren da aka fara kaiwa har ana banka wa ofishin da ake ajiyar kayan zaɓe wuta, abin damuwa ne kuma abin takaici.

Rahotanni da dama sun bayyana yadda aka yi amfani da sunƙin biredi aka babbake ofishin INEC a Ogun.

Kwana ɗaya kuma bayan harin Ogun, wasu taƙadarai sun banka wa ofishin INEC wuta a jihar Osun.

Wasu cikakkun ‘yan ta-kife sun bi daren Laraba, kafin wayewar garin Alhamis, su ka banka wa ofishin Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) wuta, a Abeokuta, babban birnin Jihar Ogun.

Ofishin da aka banka wa wutar ya na kusa da Iyaka ‘Mortuary’, cikin Ƙaramar Hukumar Abeokuta ta Kudu. ‘Yan ta-kifen da su ka banka masa wuta sun riƙa jiƙa sunƙin biredi cikin fetur, su na wurgawa a ofishin, sannan su ka ƙyasta wuta su ka tsere.

Mai gadin ofishin mai suna Azeez Hamzat, ya shaida cewa bayan an banka wutar, ya yi gaggawar kiran ‘yan sanda.

Majiya ta tabbatar cewa wasu kayayyaki da dama sun ƙone ƙurmus kafin jami’an kashe gobara su kai ɗauki.

Wakilin mu ya gano daga cikin ofisoshin da su ka ƙone, akwai ɗakin ajiyar kayayyaki, Ɗakin Yin Rajista, Zauren Shirya Taruka da sauran wasu wurare.

Kwamishinan Zaɓe na Jihar Ogun, Niyi Iyalaye ya tabbatar wa wakilin mu da wannan lamari da ya ce abin mamaki da takaici ne matuƙa.

“Amma dai yanzu mun kai rahoto wurin ‘yan sanda, kuma su na bincike,” inji shi.

Kakakin ‘Yan Sandan Jihar Ogun, Abimbola Oyeyemi ya ce bai san da labarin ba, saboda bai ƙarasa ofis ba tukunna. Amma idan ya ƙarasa ya natsu, zai yi ƙarin bayani.