Gwamna Buni ya tallafa wa marayu 200 da N50,000 kowanne

0
128

Gwamnan jihar Yobe, Hon. Mai Mala Buni ya umurci Ma’aikatar Kirkiro Hanyoyin Tattalin Arziki da Ayyukan ta baiwa zawarawa 400 tallafin dogaro da kai.

Gwamnan ya bayar da wannan umarnin ne a yau Asabar a lokacin da ya karbi bakuncin marayu 200 daga kananan hukumomi 17 dake fadin jihar.

Bugu da kari kuma, Gwamnan ya tallafa wa kowane maraya daya daga cikin adadin marayu 200 da kyautar Naira 50,000, sannan kuma shaidar da cewa sun cancanci kulawar gwamnati da sauran al’umma baki daya.

Ya ce ya zama dole a tallafa musu tare da bai wa marayu da sauran marasa galihu a nuna musu kauna ta musamman.

“Haka zalika, mun yanke shawarar tallafa wa marayun, zawarawa a cikin sauran kungiyoyi maras galihu, ta hanyar ba su jari don samun dogaro da kai.”

“Dole ne mu hada karfi da karfe don taimakawa wadanda suka rasa iyayensu, musamman wadanda rikicin Boko Haram ya rutsa dasu na tsawon shekaru goma da aka kwashe ana fama da tashe tashen hankula.”

Haka kuma, Gwamna Buni ya abawa Gidauniyar Qatar bisa tallafin kayayyakin more rayuwa ta take raba wa ga marayu da marasa galihu a fadin jihar.

A nashi bangare, Shugaban shirin kulawa da marayun, kuma mai ba Gwamnan jihar Yobe shawara na musamman kan harkokin addini, Ustaz Babagana Mallam Kyari ya yaba wa Gwamna Buni bisa yadda yake nuna damuwa da halin da marayu da zawarawa ke ciki a jihar.

“Wannan shi ne karo na biyu da mai girma Gwamna ke tallafa wa wasu marayu 200 kai tsaye da kudi.”

“Lallai wannan karimcin zai taimaka matuka wajen rage wahalhalun da ake fuskanta na yau da kullum.” In ji Ustaz Kyari.