Sojoji sun dakile harin ‘yan ta’adda, sun kashe biyu a Kaduna

0
272

Sojoji sun dakile wani hari da ‘yan bindiga suka kai musu, yayin da suka kashe ‘yan ta’addan biyu a ranar Lahadi, a garin Kankomi da ke karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna.

A wata sanarwa da kwamishinan ma’aikatar tsaron cikin gida da harkokin cikin gida Samuel Aruwan ya fitar, ya bayyana cewa sauran ‘yan ta’addan sun tsere da raunukan harbin bindiga.

Sanarwar ta ci gaba da cewa, sojojin sun samu nasarar kwato bindiga kirar AK-47 guda daya, kwarbasar alburusai bakwai, harsashi da dama da gurneti wanda aka hada da hannu guda biyar daga hannun ‘yan ta’addan.

Aruwan ya ce, yayin da aka bi sahin ‘yan bindigan wajen tserewa, sojojin sun gano gawarwakin mutane uku, bisa dukkan alamu ‘yan bindigar ne suka kashe su yayin da suke guduwa.