Wakilinmu da yaziyarci wajen ya ce wani shagon da ake sayar da biskit da alawoyi ne ya kama da wutar.
A yanzu haka dai shaguna da dama ne suka kone kurmus sakamakon gobarar da ta tashi a Kasuwar ta Singa da ke Jihar Kano.
Shaidun gani da Ido sun bayyana wa Aminiya cewa wutar ta tashi ne wajen misalin karfe 9:00 na safiyar Talata
Aminiya ta gano cewa wutar wacce ta tashi a rukunin gidaje na Mimza, ta lakume dukiya mai yawa da kayayyakin da suka hada da biskit da cingam da alawoyi da sauran kayayyaki.
Wani ganau Mai suna Hamza Isa, ya shaida wa Aminiya cewa suna zaune suna cin abinci sai suka ga hayaki na tashi daga saman benen gidan Mimza lamarin da ya sa suka yi gaggawar sanar da Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano.
“Muna zaune a kusa da gidan sai muka ga hayaki yana tashi daga gidan Mimza. Nan da nan muka fara sanar da mutanen da ke kusa da mu inda kuma ba a yi kasa a gwiwa ba aka yi gaggawar sanar da Hukumar Kashe Gobara,” inji Hamza.
Shi ma wani ganau mai suna Ado Ali ya bayyana cewa ya ga lokacin da wutar wacce ya ke kyautata zaton wutar lantarki ce ta fara tartsarsi kafin daga bisani ta kama sosai.
“Da farko mun ga tartsarsin wutar lantarki daga bisani kuma sai muka ga wuta ta fara ci daga cikin ma’ajiyar kayayyaki da ke gidan. Nan da nan muka sanar da Hukumar Kashe Gobara inda kuma suka zo suka fara gudanar da aikinsu.”
Da yake kiyasta asarar da aka yi, wani da ya sami nasarar kwashe kayansa a gidan da gobarar ta tashi mai suna Sani Musa, ya shaida wa Aminiya cewa, “Babu shakka dukiya ce ta miliyoyin kudi ta kone domin kaya ne a dankare a wurin. Kin ga saman benen can duk ma’ajiya ce ta kaya irin su biskit da alawowi da cingam. Sai kuma wani sashe da ake ajiye kayan sabulu da omo da sauran kayayyaki masu yawa.”
A karshe an yi nasarar kashe wutar gaba daya bayan da Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano ta sami taimakon wasu motocin kashe gobara daga kamfanoni masu zaman kansu da ke jihar.
Saminu Yusuf Abdullahi shi ne kakakin Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano ya tabbatar da tashin gobarar sai dai ya ce har zuwa yanzu ba su kai ga gano dalilin da ya sabbaba tashin nata ba.