Yadda Soludo ya yi wa Peter Obi wankin babban bargo

0
120
Gwamnan Jihar Anambra, Farfesa Charles Soludo, ya shawarci dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar LP, Peter Obi da ya daina mafarkin shugabantar Najeriya a 2023.

A cikin wata doguwar makala da ya rubuta wa Obin, wanda shi ma tsohon Gwamnan na Anambra ne, Soludo ya shawarce shi da kada ya yi kantafi da kuri’ar ’yan kabilar Ibo su miliyan 60.

Makalar mai taken “Tarihi alkali ne, ba zan yi shiru ba,” Soludo ya kuma ce LP ba ta da tsarin da za ta iya ja da jam’iyyun APC da PDP a Najeriya.

Ya ce, “Mu fada wa kanmu gaskiya, Peter Obi ya san ba zai iya cin zaben nan ba. Ya san wasan kwaikwayo yake yi, kuma ya san mun sani, dalilin kenan ma da ya ki komawa APGA.

“Na san zai karyata hakan, amma maganar gaskiya ita ce jam’iyyu biyu ne suke takarar nan da gaske, sauran wasan kwaikwayo suke yi,” inji shi.

Da yake tsokaci a kan yadda ya yi ta fadi-tashin ganin Peter Obi ya koma jam’iyyar APGA don yin takara a ciki domin ’yan kabilar Ibo su sami alkibla a siyasance kafin su fara neman hadin kan wasu yankunan, Soludo ya kuma yi gargadin cewa akwai yiwuwar yankin Kudu maso Gabas ta kasance babban mai da-na-sani idan Obin ya fadi zaben mai zuwa.

“A zaben Shugaban Kasa na 2019, dukkan jihohin Kudu maso Gabas sun hadu da murya daya suka goyi bayan PDP, amma gaba daya kuri’a miliyan 1.6 suka tara mata, kwatankwacin abin da Jihar Kano ta ba Buhari a zaben.

“Na san ba za su ji dadin wannan bayanin ba, amma ita siyasa lissafi ce da yin kawance da kuma hada kai da wasu har a samu nasara.

“A Dimokuradiyya, magana ake ta yawan jama’a. Har yanzu kuma ban ga ko da daya daga cikin wadannan abubuwan ba. Ida aka yi wasa, muna ji muna gani ’yan kabilar Ibo za su sake barar da damarsu a 2023 ma,” inji shi.

Daga nan sai Gwamnan na Anambra, wanda kuma tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN) ne, ya shawarci shugabannin kabilar Ibo da su tattauna da daya daga cikin manyan ’yan takarar Shugaban Kasa guda biyu kan yadda za a dawo da dauwamammen zaman lafiya a yankinsu, cikin har da yadda za a saki Nnamdi Kanu.

To sai dai da suke mayar da martani, Kwamitin Yakin Neman Zaben Peter Obi ya yi zargin cewa daukar nauyin Soludon aka yi don ya bata gwanin nasu.

Kakakin, Tanko Yunusa, ya ce, “Mu mun san abokan hamayya ne suka dauki nauyinsa domin ya yi wa tafiyarmu illa a Kudu maso Gabas. Amma abin da bai sani ba shi ne babban kuskure yake tafkawa.

“Hatta wadannan maganganun, ba komai yake yi ba face kara haskaka tauraruwar dan takararmu,” inji Tanko.