Yau 15 ga Nuwamba, jihar Kaduna ke cika shekaru 105 da kafuwa

0
121

Turawan mulkin mallaka sun dawo da hedikwatar su zuwa kaduna daga Zungeru (Dungurum) a 15 ga watan Nuwamban 1916.Yau Talata 15 ga watan Nuwamba, 2022, Kaduna ta cika shekaru 105 da kafuwa.

Gwamnatin mulkin mallaka, ta taso zuwa kaduna a ranar 15 ga watan nuwamban 1916, sai daga bisani sauran ma’aikatun dake karkashin turawan suka fara biyo hedikwatar zuwa Kaduna.

Ma’aikatar Safiyo da Baitulmali da sakatariya ta fara isowa a karshen shekara, daga nan kuma sai ma’aikatar lafiya da ta jami’an ‘yan sanda.

A cikin shekaru hudu kacal aka kammala manyan gine-gine a jihar Kaduna. An yi wadannan gine ginen ne cikin rahusa, sabida arhar aikin lebura da turawan suka samu. An kashe fam 116,150.00 wajen gina garin kaduna kafin a tare baki daya.