Bayan sake fasalin Naira, Dala na iya karye wa zuwa N200, in ji shugaban EFCC

0
146

Shugaban Hukumar Yaƙi da Cin-hanci da Rashawa ,EFCC, Abdulrasheed Bawa, ya ce dala za ta iya faɗuwa zuwa naira 200 bayan sake fasalin Naira.

Bawa ya bayyana haka ne a wata hira da ya yi da Sashen Hausa na Deutsche Welle (DW), wanda Daily Trust ta saurara, inda ya ce shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi abu mai kyau wajen amince wa da sake fasalin kuɗin.

Ya ce, “Doka ta ce za a sake fasalin takardar kudin Naira duk bayan shekara takwas amma mun shafe shekaru 20 ba tare da wani canji a kansu ba.

“Kuma hakan ya sanya kashi 85 cikin 100 na kudaden ke yawo ba a bankuna ba, a lokacin da CBN ya zo da wannan gyara, dala ta koma 880 daga baya ta koma 680 ko kusan haka.

“Don haka ka ga da wannan sake fasalin ma Naira, dala na iya faduwa sosai, wa ya sani ma ko ta kai ₦200.”

Shugaban hukumar ta EFCC ya kuma ce babu wata manufa ta siyasa a bayan wannan manufar, inda ya kuma yi kira ga ƴan Nijeriya da su kai rahoton duk wanda ya ɓoye kudade.