Gobara ta yi ajalin mutum 3 a Kano

0
112

Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, ta tabbatar da mutuwar wasu mutum sakamakon wata gobara da ta tashi a wani gida da ke yankin Yan’azara a Unguwar Kabuga ta Karamar Hukumar Gwale.

Kakakin hukumar na Kano, PFS Saminu Yusuf Abdullahi ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata.

Ya ce hukumar ta samu kiran gaggawa da misalin karfe 10:40 na safe daga wani Marwan Umar, inda ya bayar da rahoton faruwar gobarar a Kabuga ’Yan azara.

Ya bayyana cewar hukumar ta tura jami’anta daga babban ofishin kashe gobara.

“Da isarmu wurin da lamarin ya faru da misalin karfe 10:50 na safe, sai muka hangi wani gini daya mai dauke da bene biyu yana ci da wuta.

Abdullahi ya kara da cewa “Gini na biyu mai daki daya da falo, daki daya da bandaki daya shi ma ya kama da wuta.”

Wani dalibin Kwalejin Ilimi ta Tarayya (FCE) da lamarin ya faru a kan idonsa, Ibrahim Lawan, ya ce gobarar ta tashi ne daga gidan farko ta kuma tsallaka zuwa wani gida.

Ya kara da cewa rashin sanar da hukumar kashe gobara a kan lokaci ya sa gobarar ta bazu, inda ya ce mutane uku ne gobarar ta rutsa da su.

Ya bayyana wadanda abin ya shafa da suka hada da Fatima Isyaku mai shekara 16, Abdulsamad Isyaku mai shekara 15 da kuma Saddika Isyaku mai shekara 6 kacal a duniya.

Ya kara da cewa, an ceto dukkan wadanda abin ya rutsa da su, a sume wanda daga baya aka tabbatar da mutuwarsu.

Ya kara da cewa an mika gawar wadanda suka mutu ga iyayensu don yi musu jana’iza.

Abdullahi ya bayyana cewa ana binciken musabbabin faruwar tashin gobarar.