Al’Mustapha ne ya bayar da umarnin kashe mahaifiyarmu – ‘ya’yan Kudirat Abiola

0
58

Shekaru 26 bayan kisan gillar da aka yi wa marigayiya Kudirat Abiola, mai dakin marigayi wanda ya yi ikirarin lashe zaben shugaban kasa na watan Yuni 1993, MKO Abiola, ‘ya’yanta sun zargi Al-Mustapha kuma tsohon dogarin marigayi shugaban kasa na mulkin soji, Sani Abacha, bisa kitsa kashe mahaifiyarsu.

Sun yi wannan zargin ne a cikin sanarwar da Khafila Abiola ya rabawa manema labarai, inda kuma suka soki ikirarin Al-Mustapha na cewa, mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo ne, ya harzika Sajan Rogers ya bayyana sunansa a matsayin wanda ya kashe mahaifiyarsu.

A cewarsu, a zaman da aka yi a Oputa Panel a Jihar Legas, Sajan Rogers ya sanar cewa shi ne ya kashe mahaifiyarsu da Sanata Abraham Adesanya da kuma mai kamfanin jaridar Guardian, Cif Alex Ibru, bisa umarnin Al-Mustapha.

Sun yi nuni da cewa “Hujjojin da Sajan Rogers ya gabatar a Oputa Al-Mustapha da lauyoyinsa ba su iya kalulantar hujjojin ba, inda kuma babbar kotun tarayya a Jihar Legas ta yanke wa Al-Mustapha hukuncin zaman gidan yari kan yunkurin kisan Adesanya.”

Sanarwar ta ce “Babbar kotun Jihar Legas ta kuma yanke wa Hamza da sauran jami’ansa hukuncin kisa bisa hallaka mahaifiyarsu da kuma wani hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke, amma hakan bai yiwu ba, saboda wasu dalillai na ra’ayin siyasa.