Turji ya tsare yan aike bayan sun kai masa harajin N10m

0
113

Dan ta’addan nan da ya addabi yankin Zamfara da Sakkwato, Bello Turji, ya yi garkuwa da ’yan aike da suka je kai mishi Naira miliyan 10 da ya sanya wa garinsu haraji.

A ranar Talata ne Turji ya sa yaransa su yi awon gaba da biyar daga cikin mutum bakwai da suka kai mishi kudin a matsayin ‘harajin kariya,’ da ya sanya wa garin Moriki da ke Karamar Hukumar Zurmi ta Jihar Zamfara.

Wani dan garin, Sani Moriki ya ce, “Da aka shida wa Turji cewa Naira miliyan 10.5 ne kudin da aka kai ba miliyan N2o da ya bukata ba sai ya fusata, ya umarci yaransa su rike biyar daga cikin ’yan sakon su tafi da su Dajin Jirari; ko da yake biyu daga cikin mutanen sun dawo gida yau da safe.”

Sani ya ce, “Yanzu muna cikin tashin hankali kuma muna kokarin tuntubar sa kan yadda za mu kai masa cikon Naira miliyan 10 din. Al’ummarmu na cikin tsananin tashin hankali.