Dillalan kwaya 993 sun shiga hannu a Katsina

0
90
Cikin mako biyu, Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA), ta kama masu safarar miyagun kwayoyi 993 a Jihar Katsina.

Haka nan, hukumar ta ce ta kwace miyagun kwayoyi da nauyinsu ya kai kilogram miliyan 1.5 a jihar a cikin mako biyun.

NDLEA ta ce, ta kama masu fataucin da ma kwayoyin ne tsakanin ranar 10 ga Nuwamba zuwa 23 ga Nuwamba, 2022.

Kwamandan NDLEA na jihar, Mohammed Bashir ne ya shaida wa ’yan jarida cewa ingantattun dabarun aikin da suka dabbaka ne suka taimaka musu wajen samun wannan nasarar.

Ya ce, mutum 977 daga cikin wadanda aka kama din maza ne, sannan 16 mata.

Ya kara da cewa, a tsakanin lokacin da ake batu miyagun kwayoyi da suka kama sun hada da tabar wiwi da maganin tari da sauransu.