‘Yan Majalisa sun bai wa hammata iska a Saliyo

0
111

Sabani a kan wata sabuwar dokar zabe a Saliyo ya haddasa fada a tsakanin ‘yan majalisar dokokin kasar, inda suka rika bai wa hammata iska a zauren majalisar.

Abin da masu amfani da shafin twitter ‘yan saliyo suka kira hatsaniya an ga yadda ake ta kutufar juna a zauren majalisar.

An rika wurgi da sandar iko ta majalisar daga nan zuwa can.

Wani dan jarida ya ce daga nan ne kuma sai jami’an tsaro suka shiga tsakani inda suka yi waje da wasu daga cikin ‘yan majalisar.

BBC Hausa ta ce rikicin ya barke ne tsakanin ‘yan majalisar jam’iyya mai mulki da kuma na jam’iyyun hamayya a kan wani kuduri na sanya wakilci a hukumar zaben kasar daidai da karfin kowace jam’iyya a kan shirin zabukan da za a yi a shekara mai zuwa.