Shekarar 2023 za ta haifi sabuwar Najeriya – Jonathan

0
59

Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya bayyana zaben shekarar 2023 a matsayin wata dama ga ‘yan Najeriya su haifi sabuwar kasa.

Jonathan ya bayyana hakan ne a wani sakon sabuwar shekara mai taken, ‘Barka da sabuwar shekara, ‘yan Najeriya da abokan arziki a fadin duniya.

A cewar tsohon shugaban, kuri’ar ta zama abin hawa mafi dacewa don cimma “mafarkinmu” na zaman lafiya, adalci, hadin kai, da wadata.

Ya ce, “Kowace sabuwar rana kyauta ce wadda dole ne mu nuna godiya ga Allah. Muna godiya ga Allah da ya ba mu damar rayuwa, ya ba mu 2023  a matsayinmu na daidaiku da kasa baki daya.

“Ba tare da shakka ba, bara ta cika da riba da asara. A matsayinmu na kasa, mun fuskanci mummunar ambaliyar ruwa da ta yi sanadin mutuwar mutane da dama da kuma lalata dukiyoyi da hanyoyin rayuwa na miliyoyin ‘yan kasa.

“A matsayinmu na mutane, mun tsira daga bala’in ambaliyar ruwa a tsakanin sauran kalubale na kasa, muna rayuwa tare da fatan Allah da imani ga al’ummarmu, kuma mun yi nasara cikin wannan sabuwar shekara,” in ji shi.

A cikin sakon sabuwar shekara, tsohon shugaban Najeriyar ya shawarci ‘yan Najeriya da su sanya muradun al’ummar kasar a gaba a harkokinsu na bana.

Ya bayyana cewa wannan shekarar tana da damammaki masu yawa kuma dole ne ‘yan Najeriya su yi amfani da damar da suke da ita a cikin dogon lokaci da fadin kasar nan.

Jonathan ya ce, “Wannan shekarar na da matukar muhimmanci ga rayuwar al’ummarmu. Shekarar zabe ce, kuma ‘yan kasar za su fito rumfunan zabe domin zaben shugabannin mukamai daban-daban.

“Dole ne mu kalli zaben a matsayin wata dama ta haifar da sabuwar kasa da kuma shawo kan kalubalen da aka fuskanta a shekarun baya. Mu sanya maslahar al’umma a gaba a dukkan harkokinmu na wannan shekara.