An yanke wa wata mata hukuncin daurin shekara 6 kan safarar miyagun kwayoyi

0
138

Alkalin babbar kotun tarayya da ke a Jihar Legas, mai shari’a Tijjani Ringim, ya yanke wa wata mata hukuncin zaman a gidan gyran hali, na shekara shida bisa samunta da laifin safarar miyagun kwayoyi.

Ringim, ya yanke wa Fatimoh Adeoye hukuncin ne, bayan ta amsa lafin tuhumar da kotun ta yi mata na aikata laifuka biyu.

Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi (NDLEA) ce ta gurfanar da matar a kotun bisa zargin aikata lafin.

Daya daga cikin lauyoyin NDLEA, Abu Ibrahim, ya shaida wa kotun cewa, hukumar ta cafke matar ne, da kayan mayen a ranar 18 ga watan Nuwamba, 2022 a filin jirgin sama na Murtala Mohammad da ke a Ikeja a Jihar Legas.

Lauyan ya ce, an kama ta ne tana yunkurin fitar da kayan zuwa Kasar Oman.

Ya kara da cewa, laifin da ta aikata, ya saba wa sashe na 11 B na dokar hukumar da aka sabunta a 2004.

Sai dai, alkalin ya bai wa matar zabin biyan tarar Naira 500,000 kan tuhumar da kotun ke mata.