Idan aka zabi Atiku zai jefa ‘yan Najeriya cikin yunwa, zai sayar da komai – Tinubu

0
96

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Bola Ahmed Tinubu, ya gargadi ‘yan Nijeriya kan zabar Atiku Abubakar, inda ya ce dan takarar na iya jefa miliyoyin mutane cikin yunwa.

Tinubu ya yi gargadin cewa Atiku zai iya sayar da duk kadarorin Nijeriya.

A yayin da yake jawabi a yakin neman zabensa na shugaban kasa a Ilorin, a Jihar Kwara a ranar Talata, Tinubu ya ce zaben Atiku zai zama kuskure mafi girma da zai yi wuya a iya gyara shi.

Tinubu ya yi ikirarin cewa bayanai sun nuna cewa Atiku yana sha’awar zama shugaban Nijeriya ne kawai don ya wadata kansa da abokansa.

“Dan takarar jam’iyyar PDP ya shahara wajen sayar da duk wani abu da da Tarayyar Nijeriya a ta ke da su.