Ba mu sauya kudi domin yan kasa su sha wahala ba – Buhari

0
60
Buhari
Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya tabbatar wa da ‘yan ƙasar cewa gwamnati za ta tabbatar da cewa ‘yan ƙasar ba su wahala ba ta fuskar kasuwancinsu, da kuma samun tsaiko wajen musanya tsofiin takardun kuɗinsu da sabbi a yayin da wa’adin da babban bankin ƙasar ya saka ke ƙara ƙaratowa.

Yayin da yake martani game da rahotonni dogayen layukan mutanen da ke shafe sa’o’i domin samun musanya tsoffin kuɗinsu a bankuna, lamarin da ya janyo suka daga ɓangarorin adawa a ƙasar.

A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasar Mallam Garba Shehu ya fitar, shugaba Buhari ya jaddada cewa an fito da batun sauya fasalin kuɗin ƙasar ne domin yin maganin mutanen da suka ɓoye kuɗin haram, ba don cutar da talaka ba.

Ya kuma ce hakan zai magance matsalar cin hanci da rashawa da ɗaukar nauyin ta’addanci da satar mutane domin karɓar kuɗin fansa.

Shugaba Buhari ya kuma ce tsarin zai taimaka wajen ƙarfafa tattalin arzikin ƙasar

Game da wahalhalun da talakawa ke sha na musanya kuɗaɗensu kuwa, shugaba Buhari ya tabbatar da cewa gwamnati za ta yi iya bakin ƙoƙarinta domin taimaka musu wajen musanya kuɗaɗensu.

Ya kuma jaddada cewa babban bankin ƙasar da sauran bankunan ƙasar sun ƙara haɓaka hanyoyin musanya wa mutane kuɗaɗensu domin tabbatar da cewa an musanya wa kowa kuɗinsa kafin cikar wa’adin.

Babban bankin ƙasar dai ya saka ranar 31 ga watan Janairu a matsayin ranar ƙarshe ta daina amfani da tsoffin takardun kuɗi na 200 da 500 da kuma 1000 a faɗin ƙasar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here