Gwamnatin Ribas ta soke amincewar amfani da filin wasanta wajen kamfen din Atiku

0
98

Gwamnatin jihar Ribas ta janye amincewarta na amfani da filin wasa na Adokiye Amesieamaka da ke Igwurita-Ali a Fatakwal, da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar.

LEADERSHIP ta ruwaito cewa tun da farko gwamnatin jihar ta amince da amfani da filin wasan domin gudanar da yakin neman zaben jam’iyyar PDP na yakin neman zaben shugaban kasa a jihar a ranar 11 ga watan Fabrairun 2023.

Amma, Kwamishinan Wasanni na Jihar, a wata wasika da ya aike wa Darakta-Janar na Kamfen din na Atiku Rt. Hon. Aminu Waziri Tambuwal. kwamishinan ya zargi dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP da yunkurin shirya gangamin yakin neman zabe dai dai lokacin da  APC ta sa na ta.

Wasikar mai kwanan wata 31 ga Janairu, 2023 mai dauke da sa hannun kwamishinan wasanni, Barista Christopher Green, ta bayyana  cewa: “Bayanan sirri da gwamnatin jihar Ribas ke samu da kuma abubuwan da suka faru a baya-bayan nan sun nuna cewa kwamitin yakin neman zaben ku na shugaban kasa Yana aiki tare da hadin gwiwa tare da hadinkai da  wani bangare na jam’iyyar (APC) a jihar Rivers karkashin jagorancin Tonye Patrick Cole da kuma cewa manufar kwamitin yakin neman zaben ku ne na yin yakin neman zabe tare”

In za ku iya tunawa cewa Gwamna Nyesom Wike ya yi magana ne a lokacin wani gangamin yakin neman zaben gwamna na jam’iyyar PDP, in da ya zargi shugabannin jam’iyyar na kasa da yi masa bita da kulle.

Gwamnan ya ce: “Mun kama su. Su ne masu adawa da jam’iyya. Na ce musu anti-party ta haifi anti party. Kun san mun kai wadannan kananan jam’iyyu APC da SDP kotu saboda rashin yin abin da doka ta ce lokacin yakin neman zabe.

“Babu wanda zai taba mu ba tare da mun mai da martani ba. Duk wanda ya kuskura ya taba mu a Jihar Ribas, zamu yi masa dai dai da abinda yai mana. Yanzu kun nuna mana kune masu yin adawa da jam’iyya. Zamu nuna muku menene anti party. Tunda, mun kama su da hannu dumu-dumu. 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here