Harin Masallaci: Dan sanda ne ya kashe mutum 101 da bom a Pakistan

0
193

An gano cewa dan kunar bakin waken da ya kashe mutum 101 a harin bom a masallacin hedikwatar ’yan sanda a kasar Pakistan yana sanye ne da kayan ’yan sanda.

Hukumar ’yan sandan Pakistan ta sanar a ranar Alhamis cewa, “Wadanda ke gadi ba su bincike shi ba saboda yana sanye da kakin ’yan sanda… Wannan ce matsalar,” in ji Moazzam Jah Ansari, Shugaba Rundunar ’Yan Sandan Lardin Khyber Pakhtunkhwa.

Ya shaida wa manema labarai cewa ‘yan sanda sun fara gano bayanan nan kunar bakin waken ne bayan tsuntsaye jikin kansa da kuma kamanta shi da hotunan harin da aka dauka ta CCTV.

Ya yi zargin, “Akwai hadin baki,” yana mai bayyana cewa harin na ranar Litinin ba dan kunar bakin waken kadai ne ya shirya shi ba.

Daruruwan ’yan sanda ne ke Sallah a hedikwatar rundunar da ke yankin yankin Peshawar, lokacin da dan kunar bakin waken ya tayar da bom din, wanda ya da ginin ya fadi a kansu ya kashe su.

A halin yanzu dai hukumomin kasar na gudanar da bincike kan musabbabin harin a wurin da ke da tsaurara matakan tsaro a birnin da ke mazaunin hukumomin yaki da ta’addanci da na binciken kwakwaf.

Harin dai shi ne mafi muni a cikin shekaru a Pakistan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here