Hukumar JAMB za ta gurfanar da dalibai 34, ma’aikatanta na wucin gadi 6 gaban kotu

0
80

Magatakardar Hukumar Shirya Jarrabawar Shiga Jami’a (JAMB) Farfesa Ishaq Oloyede ya ce hukumar za ta gurfanar da dalibai 34 da ma’aikatan ta na wucin gadi guda shida bisa laifin hada baki da wajen dangwala yatsa ga dalibai ba bisa ka’ida ba wanda hakan ya sabawa dokar jarrabawar ta JAMB kuma doka ta bada damar hukunta wanda ya aikata irin wannan laifi.
Da yake bayyana hakan a Kano a ranar Larabar da ta gabata, magatakardar JAMB da ya je Kano domin sa ido kan yadda ake gudanar da rajistar UTME a jihar ya bayyana hakan a matsayin rashin kyautawa.
Oloyode wanda ya ziyarci shelkwatar hukumar ta JAMB da ke Mariri a karamar hukumar Tarauni ya ce hukumar ba za ta kau da kai ba wajen yin watsi da duk wata matsala da ta taso ba wajen ganin an yi almundahana a lokacin gudanar da rijista ko yin jarrabawar ba.

“Ina Kano ne domin in sa ido a kan yadda ake gudanar da rajistar jarrabawar JAMB. Ya zuwa yanzu aikin rijistar jarrabawar na tafiya yadda ya kamata kuma yana da kyau mu ci gaba da sa ido wajen maganin duk wasu ma su yin abubuwan da za su  yi domin yi mana zagon kasa”.
“Kafafen yada labarai sun ga yadda wasu a yunkurinsu na maye gurbin wasu dalibai a lokacin jarrabawa, suka rika canza hoton yatsunsu, mun ga wurare biyu zuwa uku inda muka nuna shaida kuma kusan dukkan wadanda ake zargin sun amsa laifinsu.” Inji shi.
Shugaban JAMB ya ce a maimakon yatsan daliban da suka yi rijista sai su sanya nasu sannan a karshe za su yi barazana da  tursasawa ko tilasta wa daliban su biya kudi  ko kuma yi musu barazana da duk wani abu na hasafi don sasantawa da ci gaba da aikata laifukan da suke yi, in suka ga barazanar ba za kai mu su ba.
A Kwalejin Ilimi ta Tarayya (FCE) Kano, magatakarda ya nuna alamun rashin da’a inda aka tuhumi wasu ma’aikatan wucin gadi biyu a cibiyar da yi wa wata daliba hoton zanen dan yatsa ba bisa ka’ida ba.
Ya ce dalibar ta kira wayar tarho inda ta sanarwa ’yan jarida cewa ma’aikatan wucin gadin sun buga hoton yatsan wata a madadinta.

Oloyode wanda ya jagoranci sauran ma’aikatan JAMB zuwa cibiyoyi masu manya kamar cibiyar JAMB ta Jami’ar Bayero (BUK) , Tez Computer Center, da Butale Computer Center inda ta kama hudu daga cikin ma’aikatan wucin gadi da aikata irin wannan laifin na buga yatsa ga daliban da ba su sukayi rijista ba.

Duk da cewa magatakardan ya ba su damar kare kan su akan laifin da ake tuhumar su da shi, amma wadanda ake zargin sun kasa kare kansu. Don haka ya umarci cibiyoyin da su kai su Abuja ranar Litinin inda za a mika su ga hukumar ICPC domin gurfanar da su gaban kuliya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here