Mbappe na shirin zama sabon kaftin na Faransa yayin da Varane ya rataye takalman kwallon kafa na duniya

0
54

Dan wasan gaba na Paris Saint Germain Kylian Mbappe na iya zama kaftin din Faransa yayin da dan wasan bayan Manchester United Raphael Varane ya sanar da yin ritaya daga buga kwallon kafa a ranar Alhamis.

Varane mai shekaru 29, wanda ya lashe gasar cin kofin duniya a shekarar 2018, ya zura kwallaye biyar a wasanni 93 da ya buga wa kasarsa bayan da ya fara buga wasansa a shekarar 2013.

Wasan da ya buga na karshe shi ne wasan karshe na gasar cin kofin duniya da aka yi a Qatar a shekarar 2022, inda Argentina ta doke Faransa a bugun fanariti.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here