Dakarun Faransa sun kwace makamai da Iran ta aikewa ‘Yan tawayen Yemen

0
314

Sojojin ruwan Faransa a cikin watan Janairu sun kwace dubban makamai ciki har da bindigogi da makamai masu  linzami da suka taso daga Iran zuwa Yemen, a wani ala’amari dake faruwa a baya bayannan dangane da yakin da aka kwashe tsahon shekaru ana gwabzawa.

Ita dai kasar Iran ba ta fito ta amince da wannan batu ba sai dai hotunan makaman da ake zargin na yan tawayen Houthi ne da rundunar sojan Amurka ta fitar sun nuna sun yi kama da wasu da sojojin Amurka suka kama a cikin wasu jirage mallakan Tehran.

Amurkan bata bayyana jamian da suka jagoranci aikin ba, sai dai tayi nuni da cewa sun goyi bayan kamen da sojojin ruwa na hadin gwiwa suka yi.

Sanarwar ta zo ne a daidai lokacin da kasar Iran ke fuskantar karin matsin lamba daga kasashen yammacin duniya kan jigilar jiragen yaki marasa matuka data baiwa kasar Rasha a yakin da take yi da Ukraine, da kuma murkushe masu zanga-zangar da aka dauki tsawon watanni ana yi.

Kamen ya faru ne a ranar 15 ga watan Janairu a Tekun Oman, wani ruwa da ya taso daga mashigin Hormuz, kusa da bakin Tekun Fasha, zuwa Tekun Arabiya da kuma kan Tekun Indiya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here