Hukumar kiyaye hadurra ta jihar Gombe ta ce, mutum 115 suka rasu sai kuma mutum 1,146 wadanda suka ji rauni a kan hanyoyin jihar a shekara ta 2022.
Kwamandam yanki na hukumar Mista Felid Theman,ne ya bayyana haka a zantawarsa da kamfanin dillacin labarai na Nijeriya a ofishinsu da ke Lafiyawo, karamar hukumar Akko a ranar Talatar da ta gabata.
Ya ce, an yi hatsurra guda 377 a kan hanyoyi wanda ya rutsa da mota 633 sannan kuma mutum 1,911 suka warke, haka kuma a dai wannan lokacin akwai fiye da mutum akwai mutum 765 da hatsurra suka rutsa da su amma ba su ji kwarzane ba.
Da yake kwatanta yawan hatsarin na shekara ta 2022 da na 2021, sai Theman ya ce an samu raguwar yawan wadanda suka mutu da kuma raguwar yawan hatsarin a fadin jihar.
Ya ce, a shekara ta 2021, yawan hatsarin da aka yi ya kai 438 wanda ya rutsa da mutum 2, 068 da kuma abin hawa 542, sannan kuma mutum 1,153 sun ji rauni 117 kuma sun mutu.