Canjin kudi: Buhari ya yi ganawar sirri da Emefiele

0
120

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi ganawar sirri da Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Godwin Emefiele da shugaban Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC), AbdulRasheed Bawa da Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha da kuma shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari game da halin da ake cikin na karancin takardar kudin Naira.

Kazalika gwamnan Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal da takwaransa na Jihar Kebbi, Atiku Bagudu, su ma sun halarci ganawar sirrin da aka yi a yammacin ranar Talata.

An gudanar da wannan zaman ne a daidai lokacin da ake fama da matsanancin karancin takardar kudin Naira wanda ya haddasa zanga-zanga a wasu sassan Nijeriya tare da kaddamar da hari kan wasu bankuna da jami’an tsaro.

A ranar Juma’a ne, shugaba Buhari ya roki ‘yan Nijeriya da su ba shi wa’adin kwanaki bakwai domin magance matsalar karancin takardun Naira wanda ya samo asali sakamakon shirin CBN na sauya fasalin Naira 1000 da 500 da kuma 200.

Nan da ranar 10 ga wannan wata ne, wa’adin da shugaban ya nema zai cika, yayin da mutane suka zura idanu domin ganin yadda za ta kaya.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake shirin gudanar da zaben shugaban kasa nan da ‘yan kwanaki kalilan, yayin da batun karancin Naira ya yamutsa hazon siyasar kasar nan, inda har dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu ke zargin cewa, zagon kasa ake yi masa, shi ya sa aka bullo da shirin sauya fasalin Naira gami da kirkirar matsalar karancin man fetur.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here