An yi zanga-zangar rashin Naira a wasu biranen Najeriya

0
99

Fusatattun matasa sun gudanar da zanga-zanga a jihohin Ogun da Ondo domin nuna bacin ransu kan karancin takardar kudin Naira da man fetur, inda suka kai hari kan wasu bankuna, sannan suka yi arangama da jami’an ‘yan sanda.

Masu zanga-zangar sun farfasa na’urar cirar kudi ta ATM a wasu bankuna da ke birnin Abeokuta na jihar Ogun, lamarin da ya tilasta wa ma’aikatan bankunan tserewa domin neman tudun –mun-tsira.

Kazalika ‘yan kasuwa sun rufe shagunansu a daidai lokacin da masu zanga-zangar suka fara kone-konen tayoyi tare da kokarin far wa motoci.

Wani hoton bidiyo da aka watsa a shafukan sada zumunta, ya nuna wani matashi jina-jina da aka ce, jami’an ‘yan sanda ne suka harbe shi a garin na Abeokuta.

Haka ma dai, al’amarin ya faru a jihar Ondo, inda a can ma, matasan suka gudanar da zanga-zanga duk da gargadin da ‘yan sanda suka yi musu.

Masu boren sun toshe babbar hanyar Ore da Benin, lamarin da ya haddasa cinkoson ababen hawa, abin da ya tilasta wa fasinjoji neman wata hanyar ficewa.

Ko a makon jiya, sai da aka gudanar da makamanciyar wannan zanga-zanga a garin Ibadan, kuma har matasan suka kai hari kan ofshin jami’na ‘yan sanda bayan sun fasa wani banki.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da shugaban kasar Mo. Buhari ya gana da CBN da EFCC da wasu gwamnonin kasar game da matsalar ta karancin takardar Naira a Najeriya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here