Dillalan man fetur sun lashe amansu kan shiga yajin aiki

0
134

’Yan sa’o’i bayan umartar mambobinta su rufe ilahirin gidajen man fetur a Najeriya, Kungiyar Dillalan Man Fetur ta Kasa (IPMAN) ta bukaci a bude gidajen a ci gaba da sayarwa.

Aminiya ta rawaito yadda a ranar Talata kungiyar ta bukaci a rufe ilahirin gidajen man da ke kasar nan take sannan a fara yajin aiki, kamar yadda wata sanarwa da Shugaban kungiyar na kasa, Mohammed Kuluwa, ya fitar ranar Talata.

IPMAN ta ce, “Sakamakon mawuyacin halin da muka tsinci kanmu a ciki wajen samo man da kuma sayar da shi da tsada, da kuma yadda hukumomi ke tilasta mana sayar da shi a kan farashin da muke faduwa.

“Muna umartar ilahirin mambobinmu da su dakatar da sayar da mai, sannan su dakatar da biyan kudin duk wani man da suka riga suke kokarin sarowa daga yanzu har sai abin da hali ya yi.”

To sai dai ’yan sa’o’i bayan waccan sanarwar, IPMAN ta yi mi’ara koma baya.

“Bayan tattaunawa da hukumomi masu ruwa da tsaki, muna umartar gidajen mai da su bude su ci gaba da sayarwa, yayin da uwar kungiya za ta ci gaba da tattaunawa,” kamar yadda sabuwar sanarwar ta IPMAN, wacce ita ma Shugaban nata ya sanya wa hannu ta fada.

Sanarwar ta dillalan man na zuwa ne a daidai lokacin da ’yan Najeriya ke ci gaba da kokawa da dogayen layuka da wahalar man ta haifar a fadin kasar.

Kazalika, ana fama da tsadar man a kusan duk fadin kasar, inda a wasu wuraren ya haura N370 a kan kowacce lita, yayin da a wasu Jihohin kuma rahotanni suka ce har ma ya haura N400.

Hakan kuma na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da fama da karancin takardun kudi sakamakon canjin da Babban Bankin Najeriya (CBN) ya yi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here