Ana fargabar zakulo karin gawarwaki a Turkiya da Syria

0
63

Ana ci gaba da gudanar da aikin ceto a Turkiya da Syria duk da tsananin sanyin da ake fama da shi, a daidai lokacin da alkaluma ke nuna cewa, an samu asarar rayukan mutane sama da dubu 5 sakamakon girgizar kasa da ta afka wa kasashen biyu, yayin da Hukumar Lafiya ta Duniya ke gargadin cewa, ibtila’in ka iya shafar kimanin mutane miliyan 23.

Masu aikin ceto na amfani da manyan kayan aiki a wuraren da aka samu rugujewar gine-gine sakamakon gigizar kasar mai karfin maki 7.8, inda kuma kasashen duniya ke rige-rigen kai daukin abinci da sauran nau’ukan agajin da ake bukata a kasashen biyu.

Hukumomin Turkiya sun ce, mutane dubu 3 da 549 ne suka mutu a kasar kadai, inda a Syria, adadin ya haura dubu 1 da 600, kuma ana fargabar zakulo karin gawarwaki nan gaba kadan daga karkashin buraguzai.

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta yi gargadin cewa, wannan ibtila’in ka iya shafar mutane miliyan 23, tana rokon kasashen duniya da su kara kaimi wajen agaza wa mutanen da suka tsinci kansu cikin musibar.

A bangare guda, shugaban Turkiya Recep Tayyip Erdogan ya ayyana dokar-ta-baci ta tsawon watanni uku a  larduna 10 da suka gamu da ibtila’in a kasar.

Shugaba Erdogan ya kuma ce, gwamnatinsa za ta tura sama da ma’aikatan agaji dubu 50  zuwa wuraren da lamarin ya shafa, baya ga Dala biliyan 5.3 da ya ware domin tallafa wa jama’a.

An dai bayyana girgizar kasar a matsayin mafi muni da aka gani cikin shekaru 100 a wannan yanki na duniya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here