Ba mu da takardun kuɗi da za mu buga sabbin kuɗi isassu su wadata – Emefiele

1
216

Gwaman Babban Bankin Nijeriya Godwin Emefiele ya ce CBN ba shi da isassun takardun da zai ishe su buga sababbin kuɗin da ake buƙata a ƙasar.

BBC Hausa ta ce, Mista Emefiele ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a a lokacin da yake gabatar da jawabi ga taron majalisar magabata ta ƙasar da aka gudanar a fadar shugaban ƙasar, kamar yadda wata majiya ta shaida wa Jaridar Premium Times a ƙasar.

Gwamnan Babban Bankin ya shaida wa majalisar magabatan cewa hukumar da ke lura da buga takardun kuɗin ƙasar ba ta da isassun takardun buga sababbin kuɗin, abin da ya sa aka kasa buga wadatattun takardun kuɗi da aka sabunta a ƙasar.

“Hukumar ba ta da takardun da za ta buga 500 da 1,000. Amma sun yi odar takardar daga ƙasashen Jamus da Birtaniya, to sai dai har yanzu layi bai zo kansu ba kasancewar akwai layi a odar, dan haka odarsu ba za ta samu yanzu ba”, in ji Emefiele.

Ya ƙara da cewa “CBN ya buƙaci hukumar da ke buga kuɗin da ta buga kofin takardu miliyan 70, abin da zai isa a buga naira biliyan 126 da za a sake su, su zagaya hannun mutane a wannan rana ta Juma’a, to amma hukumar ba ta da isassun takardun da za ta yi wannan aiki”. Kamar yadda majiyar ta shaida wa jaridar Premium Times.

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here